1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yanke hukuncin kisa ga wasu fursuna a Masar

Abdourahamane HassaneFebruary 2, 2015

Kotun ɗaukaka ƙara ta ƙasar ta tabbatar da hukuncin kisa ga wasu mutane 183 magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Mohammed Morsi.

Ägypten Ausweisung Journalist Peter Greste ARCHIVBILD 2014
Hoto: Khaled Desouki/AFP/Getty Images

Kotun ta ce ta samu mutanen da laifin taka rawa a lokacin da masu bore suka kashe wasu 'yan sanda guda 11 da wasu farar hula guda biyu,a Kerdassa da ke a yammacin birnin Alƙahira a cikin watan Augusta na shekara ta 2013.

A lokacin zanga-zanga da ta yi sanadiyyar kifar da gwamnatin Mohammed Morsi a cikin watan Yuli na shekarar ta 2013. A halin da ake ciki kuma wata kotun a ƙasar ta Masar ta sanar da cewar nan gaba a ranar 15 ga wannan wata. Za a sake gurfanar da tsohon shugaban ƙasar Mohammed Morsi a gaban ƙuliya a karo na fuɗu a kan laifin cin amanar ƙasa da kuma leƙen asiri.