1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a kashe masu leken asiri a Yemen

Abdul-raheem Hassan
July 9, 2019

Akalla mutane 30 ne wata kotun 'yan tawayen Houthi suka yankewa hukuncin kisa bisa zargin su da yi wa dakarun kawance da Saudiyya ke jagorantar yaki a kasar leken asiri a kasar Yemen.

Jemen Sanaa Häftlinge hinter Gittern
Hoto: Imago/Xinhua

Hukuncin kisan ya shafi malaman jami'a da jami'an kungiyar ma'aikata da masu malaman addini da ke gudanar da wa'azi a sassa daban-daban da fadin kasar Yemen.

Yanzu haka dai akwai wasu mutane shida da suka shafe shekara daya a kurkukun kasar bayan da kotun hukunta laifuka a yankin da 'yan tawayen ke da su ta yankemusu hukunci.