An yanke hukuncin sakin Tandja
November 8, 2010Wata kotun ƙungiyar haɓaka tattalin arikin ƙasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ta yi kira ga gwamnatin mulkin sojin jamhuriyar Niger da ta saki tsohon shugaban ƙasar Tandja Mamadou da take tsare da shi. Wannan sanarwar ta fito ne daga kotun ta ƙasashen Afirka ta Yamma 15 na ƙungiyar ta ECOWAS mai dakarun wanzar da zaman lafiya na kanta. Kotun mai mazauni a birnin Abujar Najeriya ta yi kira ga hukumomin na Niger da su sako tsohon shugaban wanda sojoji suka yiwa juyin mulki a cikin watan Fabrairu na wannan shekara, bayan ya ci-gaba da zama kan kujerar shugaban ƙasa watanni da dama bayan cikar wa'adin mulkinsa. A ƙarshen watan Oktoba hukumomin ƙasar sun shirya ƙuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin ƙasar, kana sun yi alƙwarin shirya sabon zaɓen gama gari a farkon shekara mai zuwa. Niger matalauciyar ƙasa dake dab da hamadar Sahara ta yi ta fama da juye-juyen mulki tun bayan samun 'yancinta daga ƙasar Faransa shekaru 50 da suka gabata.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu