Iyalan Ali Bongo za su yi zaman gidan yarin shekaru 20
November 12, 2025
Talla
An yanke wa Sylvia Bongo da Noureddin Bongo hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari saboda sama da fadi da dukiyar kasa, da halatta kudaden haram, da wasu miyagun laifuka. An kuma umarce su da su biya miliyoyin daloli a matsayin tara saboda laifukan da suka aikata a kan kasar Gabon.
Sylvia Bongo da Noureddin Bongo Valentin sun yi tasiri a lokacin shekaru 14 na mulkin tsohon shugaban Gabon Ali Bongo a tsakiyar Afirka, wanda aka hambarar da gwamnatinsa a juyin mulki a shekarar 2023 bayan ya lashe zaben da aka yi jayayya a kai wanda sojoji da 'yan adawa suka ce an tabka magudi.
Juyin mulkin ya kawo karshen shekaru 56 na daular Bongo a kan mulki.