An yankewa mutane 15 hukuncin kisa a Saudiya
December 6, 2016Wasu rahotanni dai na alakanta jagoran juyin-juya halin addinin Islama na kasar ta Iran Ali Khamenei da hannu wajen daukar nauyin masu satar bayanan zuwa kasar Lebanon dan samun horo na musamman a kan dabarun satar bayanai. A yanzu dai ana sa ran gurfanar da wasu 'yan kasar ta Saudiya 30 tare da 'yan Afganistan da Iran a kan laifukan satar bayanai nan da watannin biyu masu zuwa, sai dai kawo yanzu babu karin bayanai a kan ko 'yan wasu kasashe ne kotun ta yankewa hukuncin kisa kawo yanzu.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki matakan da kotun ta Saudiya ta dauka na yanke hukuncin kisan, inda ta ce hukuncin ya keta hakkin dan Adam. Kawo yanzu dai babu martani daga mahukuntan Tehran akan wannan hukunci, amma ana ganin hukuncin a matsayin tsamin dangantaka tsakanin kasar Saudiya da kasar Iran.