1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi ɗauki ba daɗi a yammacin Sudan

September 23, 2011

Farmakin dakarun gwamnatin Sudan ya haddasa asaran rayuka a yankin Darfur na yammacin Sudan, wanda ya yi fama da tashin hankali tun shekaru masu yawa

Dakarun kungiyar 'yan Tawayen Darfur ta SLA, bayan da suka fice a taro sasantawa da MDD ta shirya a yankinHoto: UNMIS/Tim McKulka

Dakarun gwamnatin Sudan da na ƙungiyar 'yan tawayen Darfur sun gobza a yakin dake yammacin ƙasar ta Sudan, inda ƙunigiyar 'yan tawayen SLA ta bada rahoton cewa dakarun gwamnati sun hallaka mutane bakwai a farmakin da suka kai daren jiya. Dama dai kakakin ƙungiyar 'yan tawayen Seraf Umar ya faɗawa kamfanin dillancin labaran Faransa wato AFP cewa ana ta yin ɗauki ba daɗi a yankin. Sai dai babu tabbacin labarin da 'yan tawayen suka bayar, domin ba samu jin ta bakin sojin gwamnatin Sudan ba, kana rundunar kiyaye zaman lafiya ta haɗin gwiwar MDD da Tarayyar Afirka tace, ba ta da labarin barkewar tashin hankalin. Shugaban rundunar Ibrahim Gambari a makwan jiya yace an samu raguwar tashin hankali a yaklin Darfur, don haka kimanin mutane 700 suka bar sansanin tsugunar da 'yan gudun hijira. Ibrahim Gambari yace abinda ke kawo cikas na ware ware rikicin yakin Darfur shi ne ba a iya isar wasu yankunan da ke fama da tashin hakali, sakamkon tsauraren dokokin da gwamnati ta yi da kuma dokar da mayakan 'yan tawaye suka shinfiɗa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala