1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi addu'ar neman zaman lafiya a Kaduna

January 27, 2012

Yayinda matsalolin tsaro suka dabai-baye Tarayyar Najeriya, kungiyoyin addinin Musulunci da Kisirta a jahar Kaduna sun gudanar da addu'o'i na musamman domin neman Allah ya kawo karshen tashin hankali a jahar da Najeriya

Christliche Kirche und im Hintergrund Moschee in Abuja, Nigeria. Foto: fotografiert und aus Privatarchiv zur Verfügung gestellt von Katrin Gänsler.
Babbar mujami'ar tarayya Najeriya dake AbujaHoto: Katrin Gänsler

Limaman masallatan jumma'a da pastoci tare da sarakunan gargajiya da hukumomi a garin Kaduna sun tattaru a dandalin bajakolin Kaduna, dan gudanar da addu'o'i na musanman da zumar kaucewa bala'in da suka auku a wasu jihohi makwabtan kaduna, wadanda suka shafi tashe tashen bama bamai kamar na jahar Kano da wasu jihohin kasar.

A rana Juma'a aka gudanar da da addu'o'in wadanda da gwamnatin jahar Kaduna ta ware, domin tun da karfe 6shida na safe daukacin malaman kungiyar Jama'a'tul Nasrul Islam JNI da na hadaddiyar kungiyar kiristocin Najeriya C.A.N suka tattaro wajan gudanar da addu'o'i , da zumar Allah ya kwantar da dukkanin rigingimun da suka kunno kai a Nigeria, tare da bukatar ganin cewa kowa da ya bada tasa gudunmawar a fafitikar da suke yi na ganin tarwatsewar miyagun makamai da yin fito na fito tsakanin yan kungiyin yan bindiga da jami'an tsaro a wasu jihohi makwabta basu kai ga isa Kaduna ba kamar dai yadda Revren David Joke daga kungiyar C.A.N a Kaduna ya shaidar.

Wani da harin bam ya ritsa da shi a NajeriyaHoto: dapd

"Yace dalilin wannan taron shine a gudanar da addu'o'i tsakanin musulmai da kirista da zumar tabbatar da hadin kai, mu kuma koma ga mahalatci Allah dan kawo zaman lafiya a cikin kasar mu, a sakamakon halin da jama'a suka fada a cikin ida aka samu salwantar rayuka"

Shi kuwa dakta Saidu Abdullahi shine dai wakilin shugaban kungiyar Jama'atul Nasrul Islam a wajan wannan taro,kuma yana mai cewa

" Tattaunawa da yan kungiyar Boko Haram ba wata matsala ba ce, domin an gudanar da hakan a wasu lokutan baya inda tsohon shugaban Najeriya Alhaji Umaru Musa Yar'adua ya gafartawa yan gwagwarmayar Niger Delta, a yanzu haka babu wanda ya gamsu kan yadda tabarbarwar al'amurran a cikin Najeriya ke gudana,yace halin da muke ciki,yanzu haka dole ne a koma ga Allah, mu roke shi domin samun kyakkawar zaman lafiya a ko'ina fadin kasar mu"

Jama'a na gudu lokacin tashin bama-bamai a KanoHoto: Reuters

Wadan nan tashe tashen hankula dai da suka kunno kai a Jihohin arewa na ci-gaba da gurgunta tattalin arzikin kasa,baya ga haddasa salwantar daruruwan mutane tun a shekara ta 2009 lokacin da aka fara samun fashe fashen kazaman makamai a cikin kasar,yayin da Najeriya ke shagulgulan bikin samun mulkin gashin kai.

Mawallafi: Ibrahima Yakubu

Edita: Usman Shehu Usman