An yi amfani da makamai masu guba a Siriya
December 13, 2013Wani rahoton Majalisar Ɗinikin Duniya ya tabbatar da cewa an yi amfani da makamai masu guba aƙalla sau biyar a ƙasar Siriya, kafin ta amince ta kwance ɗammara. Rahoton ya kuma ba da hujjojin cewa an yi amfani da makaman a wasu yankuna biyar waɗanda suka haɗa har da Ghouta ba Jubar.
To sai dai rahoton bai danganta hare-haren muggan makaman da kowa ba, domin waɗanda suka gudanar da binciken ba su da hurumin yin haka bisa tanadin ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar.
Tun da farko dai shugaba Bashar Al-Assad ya amince cewa dakarun shi sun mallaki waɗannan makamai, kuma ya yi alƙawarin miƙa su ga ƙwararrun ƙasa da ƙasa amma kuma ya haƙiƙance kan cewa dakarunsa basu taɓa fararen hula ba.
Gwamnatocin ƙasashen Yamma da na Larabawa da ƙungiyoyin dake rajin kare hakkin bil adama da ma 'yan tawayen Siriyan na zargin Assad da amfani da makamai masu guban a yayinda a waje guda, Assad da abokan shi da suka haɗa da Rasha da Iran ke zargin 'yan tawaye da aikata wannan ta'asa
Rahotan ya riga ya shiga hannun Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya kuma babban sakataren Majalisar Ban Ki- Moon zai gabatar da shi a hukumance ga babban zauren ranar juma'a idan an jima.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar