1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi ba ta kashi tsakanin ’yan Taliban da sojojin NATO a Afghanistan.

August 20, 2006

A Afghanistan, an yi wani mummunan ba ta kashi tsakanin mayaƙan ƙungiyar Taliban da dakarun ƙasar da kuma na ƙungiyar NATO a yankunan kudancin ƙasar, inda rahotanni ke nuna cewa ’yan Taliban 71 da kuma sojojin Afghanistan 5 ne suka rasa rayukansu. An dai yi fafatawar ne a lardin Panjwayi da ke kudancin jihar Kandahar.

A halin da ake ciki dai, ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier ya fara wata ziyarar kwana 3 a Afghanistan ɗin. Tun cikin watan Yuni ne Jamus, wadda ke da dakaru dubu 2 da ɗari 8 girke a Afghanistan, ta karɓi jagorancin rundunar NATO a arewacin ƙasar.