Bankwana da Kofi Annan a Ghana
September 13, 2018Al'ummar kasar Ghana da sauran na sassan duniya sun yi jimami a wannan Alhamis da aka binne gawar tsohon sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan a kasarsa ta haihuwa wato Ghana, bayan bikin ban-kwana da shugabanni dabam-dabam suka yi masa. Bikin binne Mr. Annan wanda aka yi da misalin karfe 8.30 na safiyar Alhamis agogon Ghana, shi ne zai kawo karshen girmamawar da kasar ta shirya masa.
Marigayin ya jagoranci Majalisar Dinkin Duniyar ce tsakanin shekarar 1997 zuwa 2006, mukamin da ya kasance bakar fata na farko da ya rike shi. Kofi Annan ya bar duniya ne a ranar 18 ga watan jiya na Agusta yana da shekaru 80, bayan gajeriyar jinya da ya yi a kasar Switzerland.
Da take jawabi a wajen bikin binne mamacin 'ya ga Annan ta bayyana mahaifinta a matsayin mutum mai saukin kai da ke jan hankali ga iyalansa su zama masu takawa da yawan godiya ga mahalicci.
Bikin binne Annan ya samu halartar manyan baki a ciki da wajen kasar ta Ghana, musamman jami'ai da ke zama na diflomasiya a wannan lokaci da lokutan baya wadanda suka rika bayyana kyawawan halaye na mamacin da ke zama gwarzo a Afirka.