An yi belin baturen Holland da a ka yi garkuwa da shi a Niger Delta
July 10, 2006Talla
Rahotani daga yankin Niger Delta mai arzikin man petur a taraya Nigeria, sun ce an yi belin baturen nan, ɗan ƙasar Holand, da yan ƙabilar Ijaw, su ka yi garkuwa da shi,ranar alhamis da ta wuce.
Kakakin opishin yan sanda na taraya, Haz Iwendi, yace Michel Los, na cikin ƙoshin lahia, kuma za su ɗanka ga hannun kampanin haƙo man petur na Westminster Dredging, da ya kewa aiki.
Opishin jikadancin Holland, da hukumomin Nigeria, sun taka rawar gani, a belin Michel Los.
Jim kaɗan bayan kamun, kakakin gwamnatin jihar Bayelsa, ya bayana cewar, al´amarin a wannan karo,ba shi da nasaba da tsahe tashen hankullan da ke wakana a yanki Niger Delta.
Kamin Los, cemma, matasa ƙungiyar MEND, sun yi garkuwa da baƙi turawa 31, masu aiki a tashoshin haƙo man petur.