An yi garkuwa da Jamusawa a Iraqi
March 15, 2007Talla
Shugaban ƙasar Jamus Horst Köhler ya roki waɗanda suka yi garkuwa da wasu Jamusawa biyu a Iraqi, su yiwa Allah da Annabin sa, su sako su. Köhler ya yi rokon ne a wani jawabi da aka yaɗa a kafofin yaɗa labarai na Jamus da kuma ƙasashen larabawa. A ranar Asabar data gabata ce wata ƙungiyar yan takife a Iraqi, a wani hoton Viodeo, ta yi barazanar kashe jamusawan biyu idan ƙasar Jamus bata janye sojojin ta daga Afghanistan ba cikin kwanaki gona.