An yi garkuwa da masu wa'azin krista a Haiti
October 17, 2021
Rahotannin daga kasar Haiti na cewa, wasu da ba a san ko su waye ba, sun yi garkuwa da wasu Kristoci Amirkawa goma sha bakwai a yammancin jiya Asabar. Amirkawan na aikin sa kai ne a kasar kuma daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su din har da yara kanana.
Rahotannin sun sheda cewa, masu garkuwan sun nemi kudin fansa na sama da dala miliyan daya a yayin da wata majiya daga Amirka ta tabbatar da labarin sace mutanen, ba ta amince tayi karin bayani kan batun ba. Daga dai farkon wannan shekarar ta 2021 zuwa yanzu, mutum kimanin 328 aka yi garkuwa da su don neman kudin fansa a Haiti.
Kasar da ke yankin caribbean na fama da talauci a sakamakon yawan aukuwar girgizar kasa mai karfin gaske da kuma rikicin siyasa musanman na baya-bayan nan da ya barke bayan kisan gillan da aka yi wa Jovenel Moise shugaban kasar a watan Yulin da ya gabata.