1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsina: An sace mutane a msallaci

Abdul-raheem Hassan
December 5, 2022

An garzaya da limamin masallacin da wani masallaci da suka ji rauni bayan da maharan suka bude wuta a kan masallacin, sannan suka yi awon gaba da wasu mutum kusan 20.

Nigeria | Polizeifahrzeuge in Kankara
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriya, na cewa 'yan bindiga sun kai hari kan wani masallaci a kauyen Maigamji tare da yin garkuwa da mutane 19 a masallacin.

Wani dan sanda ya shedawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa maharan sun bude wuta kan masallacin a daren ranar Asabar, sun kuma yi wa limamin masallacin rauni da wani masallaci guda daya.

Jihar Katsina na cikin jihohin Arewa maso yammaci da tsakiyar Najeriya da ke fuskantar matsin lamba na 'yan bindiga masu kai hare-hare don sace shanu da mutane don neman kudin fansa.