1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun sace mutane a Birnin Gwari

Binta Aliyu Zurmi
January 28, 2021

An sace mutane 30 a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Symbolbild islamistischer Kämpfer
Hoto: Fotolia/Oleg Zabielin

A jihar Kadunan Najeriya 'yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mutane 30 a yayin da suka kashe wani mutum guda a wani hari da suka kai a kauyen Kungi da ke yankin Birnin Gwari.

Da misalin karfe biyu na rana maharan suka isa kauyen a kan mashina suka shiga gida-gida suna zaban wadanda za su dauka, wani shaidan gani da ido ya ce yanzu haka kauyen na cikin zaman dar-dar.


Duk da cewar a kwai jami'an tsaro amma hakan bai hana maharan kaddamar da harin ba dama tafiya da mutanen ba tare da jami'an tsaro sun kai musu dauki ba a cewar wani mazaunin garin wanda yanzu haka aka tafi da mutum uku daga cikin 'yan uwansa.