An yi gumurzu tsakanin sojin Isra'ila da Falasdinawa
May 11, 2017Talla
Wasu daga cikin masu zanga-zangar na bangaren Faladinawa sun samu munanan raunuka bayan da sojojin suka yi maratanin kariya da harsasan roba. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ke maraba da shiga tsakaninn kasashen biyu don sake tattaunar sulhuntasu. A baya-bayannan shugaban Amirka Donald Trump ya bayyana yunkurinsa na ganin ya kawo karshen rashin jituwa tsakanin Isra'ila da Falasdinu.
A tun watan watan Afirilu da ta gabata daruruwan Falasdinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila, suka sanar da fara yajin cin abinci bisa rashin kulawa a gidajen kaso. To sai dai Isra'ila ta ce gidajen yarin kasar na cika dukkanin ka'idoji da sharuda.