An yi hatsarin jirgin kasa a Masar
August 11, 2017Talla
Kafofin watsa labarai na Masar sun ce hadarin ya faru ne a lokacin da daya daga cikin jiragen, ya tsaya kan hanya bayan ya samu wata yar guntuwar matsala. Jiragen biyu wadanda daya ya taso daga birni Alkahira zuwa Alexandria, kana daya ya fito daga Port Said a kan hanyarsa ta zuwa birnin Alexandria sun ci karo a cikin jeji.