An yi jana'izar Maragayiya Winnie Mandela
April 14, 2018Dubban mutane a kasar Afirka ta Kudu sun halarci alhinin binne Marigayiya Winnie Madikizela-Mandela wanda aka yi a birnin Soweto, wadda ta kasance daya daga cikin wadanda suka jagoranci yaki da mulkin nuna wariyar launin fata na Turawa tsiraru, kuma da safiyar wannan Asabar aka yi addu'oi ga marigayiyar wadda take zama tsohuwar matar Marigayi Nelson Mandela bakar fata na farko da ya jagoranci kasar bayan kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata.
Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar ta Afirka ta Kudu yana cikin wadanda suka nuna alhinin rasuwar Winnie Mandela wadda ake mata kirari da sunan uwar-kasa, wadda ra su kimanin makonni biyu da suka gabata. Cikin wadanda suka halarci binne marigayiyar akwai tsaffin shugabannin Afirka ta Kudu da suka hada da Thabo Mbeki, Kgalema Motlanthe gami da Jacob Zuma da manyan baki daga kasashen Afirka da sauran sassan duniya.