Za a karrama musulmi a New Zealand
March 20, 2019Talla
A kasar New Zealand a wannan Laraba an gudanar da jana'izar ta farko ta mutanen da ka aka kashe a harin ta'addanci da wani dan bindiga ya kai wasu masallatai biyu a Christchurch.
An yi Jana'izar wani dan gudun hijira dan kasar Siriya Khaled Mustafa tare da dan sa Hamza mai shekaru goma sha biyar. Dan uwansa wanda ya tsira da rauni a harin ya halarci jana'izar a kujerar guragu.
Daruruwan jama'a suka suka halarci jana'izar cikin jimami da alhini. Firaministar kasar Jacinda Ardern ta ce za yi shiru na mintuna biyu ranar Juma'a a fadin kasar domin addu'oi ga mamatan. Sannan za a yada kiran sallah kai tsaye a kafofin yada labarai domin karrama mamatan