1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira da a kara kai dauki ga yankunan girgizar kasa na Pakistan da Indiya

October 22, 2005

Sakatare janar na MDD Kofi Annan ya sake yin kira ga kasashen duniya da su kara yawan taimako ga yankunan da ke fama da bala´in girgizar kasa a Pakisan da Indiya. A cikin wata wasika da ya aikewa gwamnatocin kasashe membobin MDD Kofi Annan ya ce dole a nunawa wadannan yankuna zumunci daidai da wanda aka nuna bayan igiyar ambaliyar ruwa ta Tsunami da ta auku a tekun Indiya. Annan ya ce yawan mutane da zasu mutu ka iya karuwa fiye da yadda ake zato idan ba´a kai taimakon gaggawa ba musamman yanzu da sanyin hunturun ke karatowa. Hukumomi a dukkan yankunan Kashmir da abin ya shafa sun ce mutane kimanin dubu 79 suka mutu. A kuma halin da ake ciki kungiyar tsaro ta NATO zata aike da sojoji kimanin dubu daya ciki har da likitoci da makanikai zuwa Pakistan. Yanzu haka dai ma´aikatan ceto na kokarin kaiwa ga wasu kauyuka dake kan tsaunuka inda har yanzu ba wani taimako da ya isa can.