1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kutse kan cibiyar Nukiliya a Iran

Ahmed Salisu
April 11, 2021

Iran ta sanar da cewar an yi wa cibiyar nan tata Nukilya ta Nantanz kutse ta Intanet a wannan Lahadin kuma ta ce za ta dau dukannin matakan da suka kamata wajen ganin mayar da maratani ga wadanda suka yi kutsen.

Iran I Atomkraft I Atomanlage Natanz
Hoto: Getty Images/AFP/H. Fahimi

Shugaban shirin Nukiliya na kasar ta Iran Ali Akbar Salehi ne ya sanar da hakan ta kafar talabijin mallakin gwamnatin kasar, inda ya ce harin ya shafi bangaren rarraba wuta na cibiyar, amma dai bai haifar da wata gagarumar matsala ba said ai ya ce Tehran ba za ta daga kafa ga wadanda suka yi kutsen ba.

Wannan harin da aka kai dai na zuwa ne kwana guda bayan da Iran din ta sanar da yin gwaji na wata sabuwar nau'ra ta ingata sinadarin Uranium da ke aiki cikin gaggawa fiye da wadda take da shi a halin yanzu.

Iran dai na shan suka daga kasashen duniya da dama kan shirin nata na Nukiliya wanda ake zargin tana yinsa ne don samar da makamin kare dangi, sai dai ta sha musanta zargin.