An yi tir da kalaman shugaban Iran Ahmedinejad
December 9, 2005Talla
Jamus da sauran kasashen Turai sun fusata dangane da sabbin kalaman da shugaban Iran Mahmud Ahmedinejad yayi na nuna kyamar Isra´ila. A lokacin da ta ke ganawa da shugaban Faransa Jaques Chirac a birnin Berlin SGJ Angela Merkel ta ce ko kadan kalaman na shugaba Ahmedinejad ba abin karbuwa ba ne. Shi dai shugaban na Iran ya kwatanta Isra´ila da wata cutar cancer sannan ya ce kamata yayi a mayar da kasar ta bani Yahudu cikin nahiyar Turai. Ahmedinejad ya fadawa gidan telebijin din Iran ta El Alam cewa ta haka ne kawai za´a iya warware rikicin yankin GTT. A wasu makonni da suka wuce shugaban na Iran ya sha suka da kakkausar lafazi daga kasashen duniya a dangane da kiran da yayi na a goge Isra´ila daga taswirar duniya.