1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi wa kasar Ukraine kutse a intanet

February 1, 2024

Hukumomin kasar ba su bayyana sunayen hukumomi da kamfanonin da kutsen ya shafa ba. Amma a baya manyan hukumomin gwamnati uku sun fuskanci irin wannan kalubale.

Hoto: Denis Balibouse/REUTERS

Gwamnatin Ukraine ta ce ta gano yadda aka yi kutse ga kwamfyutoci kusan 2000 da ke kunshe da muhimman bayanai. Hukumar da ke lura da ayyukan intanet ta Ukraine CERT-UA ta ce an makalawa kamfyutocin wata tangarda da ta rikita musu ayyukansu.

Hukumomin kasar ba su bayyana sunayen hukumomi da kamfanonin da kutsen ya shafa ba. Amma a baya manyan hukumomin gwamnati uku sun fuskanci irin wannan kalubale.

Tun bayan kutsen Rasha a Ukraine, hukumomin kasar sun fuskanci hare-hare ta intanet dabam-dabam, inda jami'an gwamnati a birnin Kiev galibi ke zargin gwamnatin Rasha da wannan ta'adi. Sai dai mahukunta a birnin Moscow ba su taba cewa komai a kan zarge-zargen ba.