An yi wa mai shari'ar Amirka da ban-kwana
September 25, 2020Talla
Ruth Bader Ginsburg, wadda ta rasu a makon jiya tana matsayinta na babbar mai shari'a a kotun kolin kasar, ta rasu ne tana da shekaru 87 a duniya bayan ta fama da cutar daji.
Ta kasance mace ta farko kuma Bayahudiya da ta taba shiga cikin rukunin mashahuran mutanen da ake karramawa da wannan matsayi a Amirkar.
Marigayiyar ta sha jinjina a lokacin da take raye a kan tsayawa kan hakkin mata da ma shaharar da ta yi a matsayinta na malamar makaranta kuma alkaliya.
A tarihin Amirka dai mutane 30 ne kacal aka taba yi wa irin wannan ban kwana da girmamawa a fadar shugaban kasa.