1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi wa mutane yankan rago a Neja

Abdul-raheem Hassan
January 4, 2026

'Yan bindiga sun bude wuta kan mutane a kauyen Kasuwan-Daji inda suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu 'yan garin.

Nigeria Abuja 2021 | Amina Ahmed, Ehefrau des wegen Blasphemie angeklagten Atheisten Mubarak Bala
'Yan bindigaa sun yi wa mutane yankan rago a NejaHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Maharan sun kona kasuwar yankin da gidaje masu yawa, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun ya fitar a wata sanarwa.

Akalla mazauna garin biyu sun ce adadin wadanda suka mutu ya kai 37 kuma sun ce adadin na iya karuwa saboda wasu mutane da suka bace har zuwa ranar Lahadi ba a gansu ba. Mazauna yankin sun kuma ce har yanzu jami’an tsaro ba su isa yankin ba, lamarin da ya ci karo da ikirarin ‘yan sanda na cewa sun tura jami’ai domin neman wadanda aka sace.

Rev. Fr. Stephen Kabirat, mai magana da yawun Cocin Katolika na Kontagora Diocese inda harin ya faru, ya shaidawa kafafen yada labarai na cikin gida cewa ‘yan bindigar sun kashe fiye da mutane 40 kuma wasu daga cikin wadanda aka sace yara ne.

‘Yan bindigar dai sun shafe kusan mako guda suna zagaya garuruwan da ke kusa kafin kai harin, kamar yadda wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce saboda kare lafiyarsa. Yanzu wadanda suka tsira na fargabar su je kwato gawarwakin. "Gawarwakin suna nan a kauyen Kasuwan-Daji idan ba mu ga wani tsaro ba, ta yaya za mu je can?" Mazauna garin ya ce, an kai harin na tsawon sa’o’i uku.
Irin wadannan hare-hare sun zama ruwan dare a Najeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afirka, inda gungun 'yan bindiga da dama da ke kai hari da garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Harin na ranar Asabar a kauyen Kasuwan-Daji ya faru ne a kusa da unguwar Papiri, inda aka yi garkuwa da dalibai sama da 300 da malamansu daga makarantar Katolika a watan Nuwamba. Maharan da suka kai farmaki Kasuwan-Daji sun zo ne daga dajin National Park da ke gundumar Kabe, a cewar rundunar ‘yan sandan, inda suka yi nuni da wani yanayi da suka saba yi inda gandun dajin da aka yi watsi da su ke zama mafakar 'yan bindiga.