Ukraine na fuskantar harin yanar gizo
January 14, 2022Talla
Hukumomin na Ukraine sun ce an gaza shiga shafukan ofishin ministan harkokin waje da na agajin jin kai da sauran manyan ma'aikatun gwamnatin a ranar Juma'a(14-12-21).To amma sun ce kawo yanzu kwararru a kan sha'anin yanar gizon na kokarin gyarta lamarin. Ukraine da sauran kasashen yammacin duniya sun dade suna zargin Rasha da laifin kai harin a kan yanar gizonsu da nufin tatsar bayyanai daf da lokacin da ake kai ruwa rana tsakanin Rashar da kasashen.