1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi yunkurin juyin mulki a Chadi

January 6, 2023

Gwamnatin kasar Chadi ta ce ta yi nasarar dakile wani yunkuri da wasu suka yi na juyin mulki. Kasar ta fada cikin rudanin siyasa bayan mutuwar Shugaba Idris Deby Itno a bara.

Shugaba Mahamat Idriss Deby Itno
Hoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

Gwamnati dai ta dora alhakin abin da ya faru a jiya Alhamis ne a kan wasu hafsoshin sojin kasar da ma wasu fitattun 'yan gwagwarmayar kare hakkin bil Adama.

Ta kuma bayyana yunkurin da wata kafar ungulu ga tsarin tafiyar da mulki ta amince da shi a wani babban taron kasa da aka yi a baya-bayan nan.

Sanarwar gwamnati ta bayyana wani gungu mai mutum 11 karkashin jagorancin Baradine Berdei Targuio, shugaban kungiyar kare hakkin bil Adama a Chadin a matsayin wadanda suka kitsa wannan aniya ta juyin mulki.

A ranar takwas ga watan Disamba gwamnatin ta ce jami'an tsaro sun kama wasu daga cikin wadanda ake zargin.

Chadin dai ta fada cikin sabon rikicin siyasa ne bayan mutuwar Shugaba Idris Deby Itno cikin watan Afrilun 2022, kuma dansa Mahamat Idris Deby ya gaje shi