Firaministan Haiti ya tsallake rijiya da baya
July 30, 2024Firaminista Garry Conille na kasar Haiti ya tsallake rijiya da baya ba tare da rauni ba, lokacin da kungiyoyin masu dauke da makamai suka bude masa wuta da bindigogi masu sarrafa kansu a wani yankin babban birnin kasar na Port-au-Prince kusa da asibitin da ya kai ziyara. Majiyoyin gwamnatin sun ce lamarin ya faru da yammacin jiya Litinin.
Shi dai Conille ya zama firamnista a watan Yunin da ya gabata a kasar da ke neman murmurewa daga matsalolin kungiyoyin masu dauke da makamai da ke garkuwa da mutane da kai farmaki kan juna. Yanzu haka akwai daruruwan 'yan sandan daga Kenya da aka tura domin taimakon kasar ta Haiti cikin matakan kasashen duniya na farfado da harkokin siyasa da tattalin arzikin kasar da ke cikin rudani. Firamnista Garry Conille ya sha alwashin dawo da kasar ta Haiti cikin yanayin doka da oda.