1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi zaben raba gardama a Mali

June 18, 2023

A karon tun bayan fadawa hannun gwamnatin mulkin soja, 'yan kasar Mali sun yi zabe a wannan Lahadi. Zabe ne dai na raba gardama a kan ko a sabunta kundin mulkin.

Hoto: Getty Images/AFP/M. Cattani

'Yan kasar Mali sun kada kuri'a a zaben raba gardama da ya shafi samar da wani sabon kundin tsarin mulki, zaben da ke zama na farko karkashin jagorancin gwamnatin soja.

Kasar ta yankin yammacin Afirka dai ta shiga hannun sojojin juyin mulki ne a watan Agustan shekarar 2020.

Wasu rahotanni dai sun nuna cewa fargabar iya fuskatar hare-haren ta'addanci, ta taka rawa wajen rage yawan wadanda suka kada kuri'a a wasu yankuna a zaben na raba gardama.

Gwamnatin ta Mali karkashin jagorancin Kanal Assimi Goita mai shekaru 40, ta yi alkawarin maida kasar bisa trubar dimukuradiyya a 2024.

Mutane miliyan takwas da dubu 400 ne suka yi rajistar kada kuri'a, kuma wasu bayanan ma cewa shugaban mulkin na Soja Kanal Assimi Goita, zai nemi takara a babban zaben.