An zargi Iran da keta yarjejeniya
January 22, 2018Talla
Da ya ke jawabi ga manema labarai a birnin Brussels na kasar Beljiyam, Minista Le Drian ya ce shi da takwarorinsu na Kungiyar EU za su yi dukannin mai yiwuwa wajen ganin Iran ta mutunta yarjejeniya da aka yi da ita. Baya ga wannan, ministan ya ce za su sake jaddadawa Iran din rashin jin dadinsu game da irin katsalandan da ta ke yi a kasashen Yemen da Lebanon da Siriya wanda a cewarsa na jawo rarrabuwar kai. Ya zuwa yanzu dai Iran ba ta kai ga maida martani kan kalaman na Le Drian ba.