An zargi MDD da gazawa a Sudan ta Kudu
April 9, 2014Talla
Kungiyar ta yi kakkausar suka ga MDD bisa yadda ta yi watsi da dubban 'yan gudun hijira da ke warwatse a Sudan ta Kudu. Kungiyar ta ce jami'an MDD sun yi biris da 'yan kasar Sudan ta kudu dauke da raunuka, wasu na yashe a gefen sansanin MDD yayinda suke fiskantar tarin ruwa ruwa, wanda kuma kan iya sa su kamu da cututtuka. Kungiyar ta ci gaba da cewa, kusan za iya kwatanta sansanin na MDD a matsayin wani ramin mutuwa, domin in ba an dau matakan gaggawa ba, to wani bala'in cuta na iya barkewa. Kungiyar ta Doctors Without Borders ta bayyana aikin MDD a Sudan ta Kudu a matsayin wani abun kunya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu