1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi Rasha da harbo jirgin Malesiya 

September 29, 2016

Sakamakon bincike kan harbo jirgin MH17 na Malesiya a yankin Gabashin Ukraine ya bayyana cewa an yi amfani da makami mai linzami kirar BUK mallakar kasar Rasha wajen harbo jirgin.

Niederlande Report über MH17 präsentiert
Hoto: picture alliance/dpa/K. van Weel

An dai sake mayar na'urar da ta harba makami mai linzamin kirar BUK zuwa Rasha dauke cikin babbar motar daukar kaya da kamfanin VOLVO ya kera a cewar Wilbert Paulissen dan asalin Holland da ya jagoranci tawagar masu binciken musabbabin harbon jirgin a yankin gonaki na Pervomaiskyi da ke karkashin dakarun da ke samun goyon bayan Rasha a Ukraine. 

Tuni dai Rasha ta yi watsi da sakamakon wannan bincike wanda a cewarta akwai son kai a ciki. Mai magana da yawun gwamnati Maria Zakharova a wata sanarwa da ta gabatar, ta yi nuni da cewar wannan hanya ce da kasashen yammaci suka saba amfani da ita a kan abokan adawarsu.

Mikhail Malyshevsky mai bada shawar ne wa babban daraktan kamfanin da ke sarrafa na'urar kare makamai masu linzami na Rasha...

" Bayan gwaje-gwaje masu yawa, mun tabbatar da cewar, ba da na'urar ne aka harbo jirgin ba, bisa la'akari da yadda na'urar ta harbi jirgin dama yanayin da hatsarin ya auku. Don haka ne muke tabbatr da cewar an harbi jirgin ne daga wani yanki da ke da nisa ta kudanci". 

 

Hoto: Oleg Vtulkin

A wani taron manema labarau da suka gudanar a garin Nievwegein da ke kasar Holland, daya daga cikin jami'an Fred Westerbeke ya ce tawagarsu ta samu isassun shaidu da za ta gabatar wa kotu game da sakamakon binciken. Firaministan Australiya Malcolm Turnbull ya ce ya zama wajibi a hukunta wadanda ke da hannu a wannan aika aikan...

" Ya zamanto waji a yi adalci wa dukkan wadanda wannan hari ya ritsa da su, ba tare da la'akari da kasashen da suka fito ko jinsi ko ba, babba da yaro. Duk wanda wannan makami mai linzami na Rasha ya kashe, da sanin hukumomin kasar dole ne a biya diyyarsa. Kuma za mu cigaba da fafutukar tabbatar da wannan adalci".

 

Shima Paul Guard dan asalin kasar Ostareliya da hatsarin ya ritsa da iyayensa biyu , ya ce yana maraba da wannan sakamakon bincike, sai dai a cewarsa har yanzu akwai tambayoyi masu yawa da ke bukatar amsoshi.

" A ganina jama'a na da yawancin bayanaI, kuma ina ganin an yi ta gabatar da rahotannin game da yankin da aka yi harbin da inda ya biyo. A nawa ganin babu wani sabon abu, sai dai yana da muhimmanci aga iya adadin shaidun da suka tattara".

 

Hoto: picture-alliance/dpa/F. Ismail

Babban sakataren majalisar Dunkin Duniya a ta bakin kakakinsa Stephane Dujarric na fatan samun isassun shaidu da za su isa gurfanar da wadanda ke da hannu a kakkabo jirgin na MH 17.

" Muna da yakinin cewar sakamoko na karshe kan binciken, tare da masu bincike bangaren fasaha a karkashin jagorancin hukumar kare hadaruka ta kasar Holland  da suka gano musabbabin faduwar jirgin, za su taimaka wanjen gurfanar da masu laifin".

Binciken dai bai zo da sauki ba, kasancewar tawagar masu bincike ta kunshi masu shigar da kara da jami'an 'yan sanda 100 daga kasashe guda biyar. Jagoran tawagar Fred Westerbeke ya gabatar da sakamakon ne daga hotunan bidiyo 750 da hotuna dubu 500 da shaidu ta wayar tarho dubu 150. Kazalika an saurari ba'hasin masu gani da ido 200, daura da zirga-zirga tsakanin garuruwan Gabashin kasar ta Ukraine.