An zargi shugabannin Jamus da yin facaka da kudaden haraji
September 28, 2004A kowace shekara kungiyar dake fafatukar kare hakkin masu biyan haraji a nan Jamus ta kan yi kokarin nunawa ´yan kasar yadda hukuma take kashe kudaden haraji. A kullum kuwa alkalumman da ake bayarwa dangane da kudaden da gwamnati ke batarwa a hanyoyin da ba su dace ba sukan yi kama da juna wato kimanin Euro miliyan dubu 30. A wajen wani taron manema labarai da ta kungiyar ta kira a birnin Berlin, shugabanta Karl Heinz Däke ya bayyana yadda suka yi lissafin wadannan kudade.
"Mun samu wadannan alkalumman ne bisa bayanan da shugaban hukumar kididdiga yayi cewar ana yin tsimi na kimanin kashi 95 cikin 100 wajen kashe kudaden haraji. Wato kenan akan yi facaka da kwatankwacin kashi 5 cikin 100 na kudaden haraji. Wannan adadin kuwa yayi daidai da Euro miliyan dubu 30."
A cikin rahoton da ta bayar, kungiyar ta tabbatar da cewa gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi sun kashe kudi kimanin Euro miliyan 750 wajen gudanar da wasu ayyuka da ba su da muhimmanci. Wadannan ayyukan kuwa sun hada da aikin gina gadoji da tallafawa wani shirin telebijin na hadin guiwa tsakanin tashoshin ARD da ZDF da kuma DW. Kungiyar ta nunar da cewa kwalliya ba ta mayar da kudin sabulu ba dangane da wannan shirin, inda a halin yanzu ta janyowa kasar asarar kudi sama da Euro miliyan 20.
Tambayar da ake yi shine mai yasa aka fi yin facaka da kudaden haraji fiye da na mallakin mutum. Mista Däke ya yi nuni da cewa.
"Abin da ke jawo haka shine tunanin da ake cewar ai kudin ba nawa ba ne, shi yasa sau da yawa shugabannin ke facaka da shi ba tare da yin tunani mai zurfi ba."
A saboda haka mista Däke ya yi kira da a rika hukunta masu barnatar da kudaden haraji na talakawan kasa kamar yadda ake yi a kamfanoni masu zaman kansu.
To sai dai wannan kira bai samu goyon bayan da ake bukata daga wajen ´yan majalisar dokoki ba. Hasali ma yanzu haka wakilin jam´iyar SPD a batutuwan da suka shafi kasafin kudin kasa, Joachin Poß ya zargi shugaban kungiyar dake kare hakin masu biyan haraji ne da neman suna.