An zargi sojojin Isra'ila da laifukan yaki
February 28, 2019Talla
Wani faifan bidiyo da cibiyar bincike mai zaman kanta karkashin jagorancin hukumar kare hakkin 'dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa Falasdinawa kimanin dubu shida suka jikkata a lokacin da wasu gwanayen harbi na rundunar sojin Isra'ila suka kaddamar da harbin kan mai uwa da wabi yayin zanga-zangar. Firaministan Israilar Benjamin Netanyahu ya bayyana sakamakon binciken a matsayin yarfe da kuma kin jinin Isra'ila.