1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugabar Tanzaniya ta zargi 'yan adawa kan rikicin siyasa

December 4, 2021

Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzaniya tana zargin 'yan adawa na kasar da ta'azzara riokicin jam'iyya mai mulki.

Tansania | Präsidentin Samia Suluhu
Hoto: AP/picture alliance

Shugabar kasar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan ta zargi 'yan adawar kasar da hannu wajen zubar da kimar gwamnatinta ta hanyar nuna wa bainar jama'a rarrabuwar kai tsakanin shugabannin jam'iya mai mulki a kasar.

A cikin kausassan kalaman shugabar yayin kaddamar da aikin tashoshin jiragen ruwa na gwamnati a babban birnin kasar Dar es Salam, Samia ta ce ta na fuskantar zagon kasa daga wasu 'yan kasar tun bayan hawanta karagar mulkin kasar a watan Maris din da ya gabata biyo bayan mutuiwar tsohun shugaban kasar Marigayi John Magufuli. Shugabar ta kuma nuna rashin jin dadinta kan wadanda ke ikrarin cewar ana samun rashawa fiye da kima a gwamnatinta.

Tun bayan mutuwar shugaba Magufuli, an ruwaito cewa ana samun rarrabuwar kai tsakanin mambobin jam'iyar da ke mulki a kasar tun bayan samun 'yancin kan Tanzaniya a shekarar 1961 saboda sauyin da ta kawo wanda suka sha bambam da na tsohun shugaban da ake yi wa lakabi da Bulldozer saboda salon shugabancinsa.