An zargi 'yan Jihadi da bata sunan Islama
August 19, 2014Babban limamin Saudiya ya bayyana a ranar Talatar nan cewa addinin Islama ba shi da manyan makiya kamar masu kaifin kishi da akida irin ta al-Qaida da dakarun IS domin Musulmai su ke fara cutuwa da ayyukansu.
Mufti Sheik Abdul-Aziz Al-Sheik da yake wa jamaa bayani yace taaddanci bashi da gurbi cikin addinin Islama, kuma babbar barazanar da suke da ita, ita ce suna amfani da wasu kalmomi na addinin Islama wajen aiwatar da ayyukansu na rarraba kan musulmi.
Tuni dai Sarki Abdallah na Saudiyyar ya yi ta kira ga babban malamin da ya fito fili ya yi Allah wadai da ayyukan masu kaifin kishin addinin na Islama tun bayan da gwamnatin ta haramta shiga fada ga 'yan kasar a rikicin kasashen waje.
Ya zuwa yanzu dai duk wasu malaman addini da suka ki yin Allah wadai da ayyukan na masu kaifin kishin addinin Islama a waazin su na jumaa-jumaa a kasar ta Saudiyya na iya fiskantar wasu matsaloli da suka hadar da kwace musu lasisi na yin waazi.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mouhammadou Awal Balarabe