1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana bincike kan barazanar sake kai hari a Jamus

December 22, 2024

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya isa birnin Magdeburg, inda ya shiga cikin wani taron addu'o'i na musamman domin jimamin kisan mutane biyar da wani mutumin Saudiyya ya yi ajalinsu.

Hoto: Ebrahim Noroozi/AP Photo/picture alliance

Lamarin da ya faru a yammacin ranar Juma'a ya jefa gaba daya Jamus cikin jimami, inda a wannan Asabar shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da ministar kula da harkokin cika gida Nancy Faeser da gwamnan jihar Saxony-Anhalt, inda lamarin ya faru  Reiner Haseloff, suka sauka a garin na Magdeburg domin jajanta wa iyalan mutanan da lamarin ya ritsa da su.

Sabon labarin da ke shigowa na cewa akwai karamin yaro dan shekaru tara cikin mutane biyar da mutumin ya yi ajalinsu bayan da ya bi ta kansu da mota. Hukumomi sun ce har kawo yanzu ba su gano dalilin mutumin na kai wannan hari ba. Kamfanin dillancin labaran Jamus DPA ya ce shekara guda da ta wuce  mahukumtan Saudiyya sun gargadi gwamnatin Jamus da ta sanya ido kan maharin, amma hukumomin Berlin ba su yi komai a kai ba. Majiyoyin tsaro a Saudiyyar sun ce maharin dan shi'a ne da ya fito daga yankin  Al-Hofuf i da ke gabashin kasar.