1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mabiya addinin Kirista na bukukwan Kirismeti

Abdoulaye Mamane Amadou
December 25, 2022

Kamar kowace shekara miliyoyin mabiya addinin Kirista daga sassa daban-daban na duniya, na gudanar da bukukuwan Kirsimeti a wannan Lahadi don tunawa da Yesu Al-masihu.

Mabiya addinin Kirista na ibada a Bethlehem
Mabiya addinin Kirista na ibada a Bethlehem Hoto: Mussa Issa Qawasma/REUTERS

A wannan Lahadi kamar kowace shekara mabiya addinin Kirista a fadin duniya na gudanar da shagulgulan bikin na Kirsimeti domin karrama ranar haihuwar Yesu Al-masihu. Ana gudanar da addu'o'i da ziyarar 'yan uwa da abokan arziki har ma da raba kyaututtuka domin karfafa zumunci da dangantaka tsakan mabiya addinin Kirista, wasu kuma na kara fadada dangantaka tsakaninsu da sauran mabiya addinai daban-daban a fadin duniya.

Ziyara a birnin Bethlehem 

Mabiya addinin Kirista a BethlehemHoto: Wisam Hashlamoun/AA/picture alliance

Baki yan yawon shakatawa da bude ido fiye da dubu 700 ake hasashen sun ziyarci yankin da aka haifi Annabi Isa (AS) "Bethlehem" da ke yankin Falasdinu, daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, in ji Rola Maayah, Ministar harkokin yawon bude ido ta gwamnatin Faladinu, lamarin da ya sha bam-bam da shekaru biyu da suka gabata da wuraren suka kasance a rufe saboda matsalar annobar Corona.

Karin Bayani: Karin bayani kan tushen bikin Kirisimeti

Birnin ya dau harami, ya kuma cika makil da masu ziyara, titunan yankin sun kasance cike da kwalliya, ana gudanar da wasanni masu ban sha'awa ga yara.

Sakon Fafaroma Francis daga St Peter a Vatican

Fadar Vatican Fafaroma Francis na addu'o'in Kirismeti a ranar 24.12.2022Hoto: Andreas Solaro/AFP/Getty Images

Kimanin mabiya dubu bakwai ne suka halarci addu'o'in dare da babban limanin na darikar Katolika na duniya  Fafaroma Francis ya jagoranta a daren jiya, daren da ke zama na kololuwar soma bukukuwan zagayowar haihuwa Yesu Almasihu. A sakonsa a gaban mabiyan Fafaroma Francis ya ce ya damu da tasirin yunwa da neman kudi da iko.

Ana hasashen dubun-dubatar al'umma mabiya su halarci dandalin St Peter a Vatican a wannan Lahadin mai matukar muhimmanci, domin sauraron wani sakon Fafaroma Francis ga mabiya addinin Kirista, kana a jawabinsa, ana sa ran jagoran darikar ta Katolika ya karkata kan batun yakin da ake a Ukraine da ma illolin da ke tattare da shi ga al'ummar duniya, kana kuma a jawabinsa, Fafarorma Francis zai tabo wasu batutuwan da suka ja hankalin duniya.

Shugaban Steinmeier ya bukaci kwanciyar hanakali a Ukraine

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier Hoto: Tobias Schwarz/AP Photo/picture alliance

Shugaban Frank-Walter Steinmeier ya yi kira da a samar da zaman lafiya game da yakin da ake gwabzawa a Ukraine a cikin wani jawabinsa ga al'ummar Jamus da za a wallafa nan da gaba a albarkacin wannan rana ta bukukuwan kirismeti.

Shugaba Steinmeier ya ce burinmu shi ne ganin an dawo da zaman lafiya mai dorewa, mamamyar da Rasha ta kaddamar a Ukraine ya haifar da mummunan illa da fargabar zama cikin yanayi mai matukar wuya.

Duk da yake yakin ya haifar da mummunan gibi musamman ma ga fannin tattalin arzikin Jamus, shugaban ya ce gwamnatin kasar ta bullo da wasu fasahohin rage radadin haka ga al'umma musamman ma ta fannin makamashi.

Karin Bayani: Shekara ta 2022: Bikin Kirsimeti 


Daga karshe shugaban kasar ta Jamus ya bukaci daukacin masu jini a jika da ke a matsayin manyan gobe, har ma da 'yan mazan jiya da su jajirce don yaki da gurbatar muhalli.