1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Ana ci gaba da barin wuta tsakanin Isra'ila da Iran

June 21, 2025

An shiga mako na biyu a fada tsakanin Tehran da Tel Aviv a yayin da aka wayi garin Asabar da sabbin hare-hare.

Sararin samaniyar Tel Aviv
Sararin samaniyar Tel AvivHoto: Mussa Issa Qawasma/REUTERS

Rahotanni da ke fitowa daga birnin Tel Aviv na Isra'ila sun nuna cewa Iran ta yi ruwan makamai masu linzami kan wasu yankunan kasar da suka hada da Holon inda aka hangi wuta na tashi da asubahin Asabar.

Ita kuma Isra'ila cibiyar nukiliya ta Isfahan ce da kuma wasu yankuna ta yi wa luguden wuta a jerin hare-hare da ta kaddamar kan Iran a yau din.

Wani babban jami'in sojin Isra'ila ya yi gargadin cewa za a kwashe lokaci mai tsawo ana fafatawa tsakanin kasashen biyu da ke kallon juna a matsayin abokan gaba.

Iran ta yi ruwan makamai masu linzami kan Isra'ila

Ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Saar ya yi ikirarin cewa kaddamar da farmaki da kasarsa ta yi kan Iran ya kawo mata jinkirin shekara biyu wajen kera makamin nukiliya.

'Yansandan Iran sun sanar cewa tun daga 13 ga watan Yuni an kama mutum 22 a lardin Qom bisa zargin yi wa Isra'ila leken asiri.

A wani labari mai alaka da rikicin na Iran da Isra'ila kuwa, Ministan harkokin wajen  Iran ya isa birnin Santanbul na Turkiyya a yau Asabar a cewar kamfanin dillancin labarai na Tasnim.

 Abbas Araghchi ya je Turkiyya ne domin wani taro da kasashen Larabawa suka shirya kan ci gaba da barin wuta tsakanin Isra'ila da Iran.

Iran-Isra'ila: Wace ce ke aikata fada ba bisa doka ba?

Ana sa ran jagororin diflomasiyya kusan 40 ne za su hallara a taron da zai gudana a karshen mako bisa bukatar Kungiyar kasashen Musulmi ta OIC.

Taron ya kuma zo ne bayan ganawar Araghchi da takwarorinsa na Burtaniya da Faransa da kuma Jamus a birnin Geneva a ranar Juma'a.

A ranar 13 ga watan Yuni ne dai Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a kan Iran inda take zarginta da kokarin kera makaman nukiliya, zargin da Iran ta ce ba shi da tushe bare makama.