1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da fafatawa a ƙasar Libiya

March 12, 2011

Bisa ga dukkannin alamu ba a cimma tudun dafawa ba a taron gangami na ƙasashen Larabawa a birnin Alƙahira

Tutar ƙungiyar ƙasashen LarabawaHoto: DW

Ƙungiyar ƙasashen Larabawa wacce yanzu haka ta ke gudanar da wani taron gaggawa a birnin Alƙahira na ƙasar Masar ta amince da haramta wa jiragen yaƙin Libiya shawagi a sararin samaniyar ƙasar.

Ministocin harkokin waje na ƙasashen Larabawan waɗanda suka yi baki ɗaya domin gayyatar kwammitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniyar da ya zartas da hukumcin akan ƙasar ta Libiya

sun gamu da adawar wasu ƙasashe irinsu Algeriya da Siriya da ba su yarda ba da shirin.

Ƙungiyar dai ta ce za ta buɗe shawarwari da majalisar ƙasa ta wucin gadi da 'yan adawar suka girka wato CNT domin samun damar taimaka wa al'uma Libiyar.

Yanzu haka kuma faɗa na ci gaba da ƙara yin ƙamari a fagen daga inda dakarun kanal Gaddafi ke ci gaba da kai farmaki domin sake ƙwace iko a garin Misrata, garin na ukku mafi girma mai tashar man fetre daga hannu yan tawaye wanda tuni suka riga suka ja baya daga birnin Ras Lanuf tun can da farko.

Mawallafi: Abdurrahaman Hassane

Edita: Ahmad Tijani Lawal