1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan kasashen waje na ficewa daga Sudan

Ramatu Garba Baba
April 22, 2023

Saudiyya da wasu kasashen yamma na rige-rigen fitar da 'yan kasashensu daga Sudan a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada a Khartoum babban birnin kasar.

An ci gaba da gwabza fada a Sudan
An ci gaba da gwabza fada a SudanHoto: Iraqi Foreign Ministry/Reuters

Rundunar sojin Sudan ta ce, ta soma kokarin ganin an fitar da jami'an diflomasiya na kasashen yamma daga cikin kasar a yayin da ake ci gaba da gwabza fada a Khartoum babban birnin kasar. Shugaban kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ce, ya bai wa shugabanin kasashen Amirka da Britaniya da Chaina da Faransa tabbacin fitar da 'yan kasashensu daga cikin kasar cikin koshin lafiya.

Mutum sama da dari hudu rahotanni ke cewa, sun mutu a kasar, tun bayan barkewar kazamin fada a tsakanin dakarun sojin Sudan na bangaren shugaban kasar Janar al-Burhan da na shugaban rundunar RSF da Janar Hamdan Dogalo ke jagoranta.