Ana ci gaba da jan kunnen Koriya ta arewa akan barazanar gwajin nukiliya
October 4, 2006Talla
Kasashen duniya suna ci gaba ta maida martani da kakkausar murya game da barazanar da Koriya ta arewa tayi na gwajin nukiliya.
Kasar Amurka tace yin hakan wani neman tsokan ne a bangaren Koriya ta arewan kuma zata iya ganin mummnunan sakamakonsa.
Kungiyar taraiyar Turai,Japan da Sin sun bukaci Pyongyang data daure kada tayi wannan gwaji domin kare tsaron yankin.
Koriya ta arewan wadda bata baiyana takamammen loacinda zatayi gwajin ba tace,zatayi ne saboda gaba da amurka take nuna mata.