1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da kame-kame a kasar Turkiyya

Mouhamadou Awal Balarabe
December 17, 2019

Amfana da wata manhaja ya ce hukumomi sun kama mutane da dama a Istanbul da sauran sassa na Turkiyya bisa zargin marar hannu a yunkurin juyin mulki na 2016.

Türkei Symbolbild Polizei
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Tazegul

Hukumomin Turkiyya sun kama mutane sama da 181 bisa zarginsu da marar alaka da kungiyar Gülen da ake zargi da kitsa juyin mulki da bai yi nasara ba shekaru uku da suka gabata. Ofishin babban mai shigar da kara da ya bayar da wannan sanarwa ya ce wadanda ke tsaren sun yi amfani da wata manhaja da magoya bayan Gülen suka samar wajen aika wa da sako a yayin yunkurin juyin mulki. 
 
Shi dai Fetullah Gülen shehun malamai dake gudun hijiara a Amirka na sahun gaba na wadanda Recep Tayyip Erdogan ke zargi da zama kanwa uwar gami na neman hambarar da gwamnatinsa ta hanyar da ba ta dace da dimukaradiyya ba, lamarin da ya karyata. Mutane dubu 50 hukumomin Turkiyya suka kama tare da korar ma'aikata dubu 140 daga bakin aiki bisa zargin mara wa yunkurin na juyin mulki baya a shekara ta 2016.