1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Zaben Amirka ya dauki hankalin duniya

Suleiman Babayo ZMA/LMJ
November 4, 2020

Ana ci gaba da jira sakamakon sauran jihohin da suka rage domin sanin wanda ya lashen zaben shugaban Amirka.

US Wahl 2020 Japan Börse
Hoto: Carl Court/Getty Images


A kasar Amirka ana ci gaba da kirga domin tantance mutumin da zai lashe zaben shugaban kasa tsakanin Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican da babban mai adawa da shi  Joe Biden na jam'iyyar Demokrat.

Kalilan na jihohi suka rage amma su ne za su tantance gwani tsakanin 'yan manyan 'yan takaran wadanda kowanne yake yunkurin kai wa ga gaci, na samun yawan kuri'un wakilan masu zaben shugaban kasa. Duk dan takara da ya samu yawan wakilan da ke zaman shugaban kasa 270 shi ne zai zama shugaban kasa na gaba, kuma dan takara zai iya samu idan ya lashe galibin wakilan da aka raba tsakanin duk jihohin kasar 50.

An samun tsaikon saboda yadda ake ci gaba da kirga milyoyin kuri'u na mutanen da suka yi zabe ta hanyar aikewa da wasiku, sakamakon annobar cutar coronavirus, kawo yanzu akwai jihohi kusan 10 da suka rage.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani