Ana ci gaba da kokarin shawo kan rikicin Israela da Lebanon
August 4, 2006Talla
A ranar litinin ne idan mai duka ya kaimu ake sa ran ministocin harkokin wajen kasashen larabawa zasu gudanar da wani taron gaggawa, a birnin Cairo na kasar Masar.
Taron a cewar, mataimakin shugaban kungiyyar,Ahmed Ben Helli, zai tattauna rikicin dake tsakanin Israela ne da kuma kungiyyar Hizbullah.
Ko da a yau juma´a sai da jiragen yakin sama na Israela suka kai wasu hare hare a kudu da kuma arewacin birnin Beirut, wanda hakan yayi sanadiyyar rasuwar mutane fararen hula 40.
A waje daya kuma, dakarun kungiyyar Hizbullah sun shaidar da harba rokoki sama da dari izuwa arewacin kasar Israela a yau din nan, wanda hakan yayi sanadiyyar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama.