Akwai takaddama kan zaben shugaban kasar Burundi
July 7, 2015![Burundi Imbonerakure Miliz](https://static.dw.com/image/18558385_800.webp)
Talla
Shugabannin kasashe masu makwabtaka da Burundi sun bukaci jinkirta zaben shugaban kasar da makonni biyu. Haka ya zo yayin da ake fama da tashe-tashen hankula kan shirin Shugaba Pierre Nkurunziza na sake neman mulki a wa'adi na uku.
An tsara zaben shugaban kasar ranar 15 ga wannan wata na Yuli, gwamnatin Nkurunziza tana nuna adawa da shirin jinkirta zaben. Shugabannin kasashen Gabashin Afirka sun nemi a kafa gwamnatin hadin kan kasa. Shugabannin sun nada Shugaba Yoweri Museveni na Yuganda da ya shiga tsakanin gwamnatin Burundi da 'yan adawa.