1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci- gaba da samun tashe tashen hankula a yankin Gabas ta tsakiya

June 22, 2011

ƙasar Siriya ta yi kashedi ga ƙasar Faransa da shiga cikin harkokin cikin gidan ta yayin da kuma a can ƙasar Yemen 'yan adawa ke kokarin canza mulki

Masu zanga zangar neman sauyiHoto: AP

►Ƙasar Siriya ta gargaɗi ƙsashen duniya musamman ma dai ƙasar Faransa da yin katsa landan kan boren ƙin jinin gwamnati da ya dabaibaye ƙasar. Ministan harkokin wajen ƙasar ta Siriya Walid al-Muallem ne ya yin wannan gargaɗi a wani jawabi da ya yi ga manema labarai a Damuscus.

Ministan harkokin wajen na ƙasar ta Siriya ya ce sam ƙasar su ba za ta lamunci duk wani katsa landa kan rigingimun da su ka dabaibaye ƙasar daga kowacce ƙasa ba domin kuwa rikicin su na cikin gida wanda za su iya magance kayansu ba tare da wata ƙasa ta tsoma mu su baki ba.

Ministan ya ƙara da cewa babu wata ƙasa da za ta zana mu su hanyoyin da za su bi wajen warware banbance-banbancen da ke tsakanin gwamnati da waɗanda ba sa ga muciji da ita, kazalika ya yi kira ga Turkiyya wadda ke ɗaya daga cikin ƙsashen da ke rajin ganin an kawo sau a ƙasar kuma ta wasu 'yan ƙasar ta Siriya mafaka da sake tunani.

Yayin da ministan harkokin wajen na Siriya ke wannan batu, a gefe guda kuma ƙungiyar Tarayyar Turai sake ƙaƙabawa ƙasar takunkumi ta yi baya ga wanda aka sa a watan Mayun da ya gabata kan wasu manyan jigajigan gwamnatin ƙasar su sha bakwai da ma dai hana taɓa wasu kuɗaɗe da ƙasar ta ajiye a wasu bankunan wasu ƙasashen Turai. Wannan sabon takunkumin da aka sanya dai ya kawao yawan mutanen da ƙungiyar ta Eu ta sa wa takunkumi zuwa 34, al'amarin da ƙasar ta Syria ta yi Allah wadai da shi inda ta bayyanar cewar hakan tamkar fito na fito da ƙasar musamman dai abin da ya danganci tattalin arzikin ƙasar.

A ƙasar Yemen kuwa wadda ita ma ke fama da bore irin na ƙin jinin gwamnati wanin babban hafsan sojan ƙasar ne da wani shugaban wata al'umma su ka yi kira ga mataimakin shugaban ƙasar Abdrabh Mansur Hadi da ya ɗare kan karagar mulkin ƙasar ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Janar Ali Mohsen da Sheikh Sadiq al-Ahmar su ka ce ka ce kyautuwa yai mataimakin shugaban ƙasar ya haye gadon mulki domin ci-gaba da jan akalar gwamnatin ƙasar tare da yin alƙwarin bashi dukannin irin goyon bayan da ya ke buƙata wajen gudanar da aikin sa. Masu sharhi kan al'amuran da ke wakana a ƙasar dai na ganin ɗarewar mataimakin shugaban kan karagar mulkin ƙasar na iya cin karo da babban ƙalubale kasancewar har kawo wannan lokacin waɗanda ke biyayya ga Shugaba Ali Abdallah Saleh ne riƙe da dama daga cikin madafun ikon ƙasar musamman ma dai rundunar sojin ƙasar wadda ɗan Shugaba Saleh ke jagoranta.

A ƙasar Libya kuwa, yunƙurin maƙalewa kan kujerar shugabancin ƙasar da Shugabanta Mu'ammar Ghaddafi ke yi ne ya fuskanci koma baya sakamakon hawa teburin tattaunawa da gwamnatin ƙasar sin ta yi da 'yan tawayen ƙasar ta Libya a wata ziyara da su kai ƙarƙashin jagorancin wani jigo a a ɓangaren na 'yan adawa Mamoud Jibril.

Ministan harkokin wajen ƙasar Sin Yang Jiechi ya ce ƙasar su ta ɗauki 'yan adawar da matuƙar mahimmanci, wannan bayanan na Mr. Jiechi dai na ya zuwa ne jim kaɗan bayan da wani farmaki da dakarun da ke biyayya ga shugaba Ghaddafi su ka kai garin Misrata, harin farko a da dakarun na Ghaddafi su ka kai a cikin makwannin baya-bayan nan.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal