Ana ci gaba da tashe-tashen hankulla a Bangui
May 30, 2014Masu zanga-zangar dai na nuna kyamar su ce ga shugabar rikon kwaryar kasar Catherine Samba Panza, da ma dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa dake ayukan tsaro a wannan kasa.
Daga nasu bengare kungiyoyin mayaka da suka ki su ajiye makammai a wannan kasa, na kai hare-hare ga dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa, a duk lokutan da motocin su ke fucewa cikin birnin Bangui, inda su kuma suka sha alwashin mayar da martani.
Harin baya-bayan nan dai da wasu 'yan bindiga suka kai a wani Coci dake birnin na Bangui, inda aka kashe mutane 17 tare da yin awon gaba da wasu mutanen 27 ne, ya kara tayar da kayar bayan masu zanga-zangar, Inda a wannan Juma'ar ma shugabar kasar ta rikon kwaryar Catherine Samba Panza, tayi Allah wadai da harin da tace na ta'adanci ne.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar