1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben Ghana

December 8, 2020

Hukumar zaben Ghana na ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a jiya Litinin inda takara ta fi zafi tsakanin shugaba mai ci Nana Akufo-Addo na NPP da tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama na NDC.

Afrika Ghana Präsidentschaftswahlen
Annobar corona ta rage wa zaben armashiHoto: Xu Zheng/Xinhua News Agency/picture alliance

A wannan Litinin 7 ga watan Disamba ne jama’ar Ghana ke yin zaben shugaban kasa dana 'yan majalisa bayan shekaru 4 na wa’adin kowace gwamnati mai ci ya zo karshe. Akasin yadda aka saba da ganin dogayen layuka ko kuwa wasu jama’a su saka duwatsu ko wasu abubuwa domin kama wa kansu gurbi a layi, zaben na bana za a iya cewa ya rasa armashinsa, don kuwa babu jama’a sosai kamar yadda aka saba gani. Wakiliyarmu Jamila Ibrahim Maizango, ta zagaya ya zuwa rumfar zaben city Engineers da ke mazabar Odododiodio da ke cikin birnin Accra, inda jama’a ke tayar da jijiyoyin wuya a game da zargin wasu da ba su fito da wuri ba amman suke kokarin shige gabansu. Karin bayani:Ko shugaba Akufo ya cike alkawura a Ghana?'Yan takara kimanin goma sha biyu ne ke zawarcin kujerar shugaban kasar, amma takarar zai fi zafi a tsakanin manyan jami'iyyun NPP da NDC wato Shugaban kasar mai ci a yanzu Nana Dankwa Akufo Addo mai shekaru 76, da kuma tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama mai shekari 62 daga jam'iyyar NCD. Sai dai ana bukatar kowane dan takara ya samu kuri'u sama da kashi 50 don gudun shiga zagaye na biyu. 'Yan takara 918 ke takarar kujeru 275 a majalisar dokokin kasar, kuma sama da 'yan kasar miliyan 17 suka yi rejistar zaben da za a yi mazabu sama da 38,000. Shugabanin biyu wato tsohon Shugaban kasar John Mahama da Shugaba mai ci yanzu Akufo-Addo sun sha alwashin tabbatar da zaman lafiya, yayin zaben da ma bayan kammala shi. Tsohuwar shugabar Liberia Hellen Johnson Sirleaf da wakilin musamman na sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya a yankin yammacin Afirka da Sahel duk sun mika sakonninsu dangane da muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da guje wa tashe-tashen hankula.

Annobar corona ta rage wa zaben armashiHoto: Xu Zheng/Xinhua News Agency/picture alliance