1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da yin aikin agaji a Iran

August 12, 2012

Masu aikin ceto na ci gaba da zaƙulo mutane da suka maƙale a cikin ƙuraguzan gine gine da suka ruguje a sakamakon tagwayen girgizar kasar.

pictures of Iran earthquake in Ahar (zugestellt von Hossein Kermani) Keine BILDBESCHREIBUNG, daher REUTERS-TEXT: Dubai, 11. Aug (Reuters) - Zwei schwere Erdbeben haben am Samstag den Nordwesten des Irans erschüttert. Die Beben in der Nähe der Stadt Tabris hatten US-Geologen zufolge eine Stärke von 6,4 beziehungsweise 6,3. Die iranische Nachrichtenagentur Fars berichtete, Bewohner seien aus Angst aus ihren Häusern auf die Straßen geflüchtet. 50 Verletzte seien in Krankenhäuser gebracht worden. Berichte über Todesopfer lagen zunächst nicht vor.
Hoto: MEHR

Masu aiko da rahotannin sun ce sama da mutane 200 aka ceto a cikin tarkacen gine gine da suka zube a garuruwan Varzaghan da Ahar, inda aka girka wani asibiti na gauggawa da ke karɓar jama'a:

Girgiza ƙasar mai ƙarfin maki 6.3 a maunn Richter, ta share ƙauyuka guda shidda ɗungurun gum, yayin da kashi 50 na wasu ƙauyukan guda 60 suka lallace.Mutane kusan 250 ne suka mutu, kana wasu dubu ɗaya da ɗari biyar, suka jikata,sannan ana gani cewar addadin waɗanda lamarin ya rutsa da su zai iya ƙaruwa a nan gaba.Hukumomin sun gargaɗi jama'a da su ficce daga gidajan su,saboda yiwar aukuwar ƙarin girgiza, wacce ta tilasa wa mutane dubu 16 ƙaurace wa muhalin su.

Mawallafi:Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal